'Yan sanda sun tabbatar da babu sauran guba a filin jirgin sama

Masu bincike a filin jirgin sama na Kuala Lampur
Image caption An dai tsaurara matakan tsaro a filin jirgin saman da lamarin ya faru

Jami'an tsaro a kasar Malaysia sun sanar da cewa babu wani hari da mutane ka iya fuskanta a filin jirgin saman Kualar Lampur, wurin da aka hallaka dan uwan shugaban Koriya ta Arewa kusan makwanni biyu da suka gabata.

Tun da fari 'yan sanda sun bincike lungu da sakon filin jirgin dan neman ragowar guba mai saurin kisa da aka yi amfani da ita da sauran sinadarai masu hadarin gaske, wanda da su aka yi amfani wajen kisan Kim jung-Nam.

Daya daga cikin matan da ake zargi sun shafawa marigayin gubar a fuska, ta ci gaba da kafewa ba ta da hannu a kisan, kuma an bata dala 90 bayan an yaudare ta da cewa man da aka bata na cikin roba na jarirai ne.

Masu bincike sun sanar da cewa matan da ake zargi da hannu a kisan Kim Jung-Nam, sai da aka ba su horon yadda za su shafawa mamacin guba a fuska da kuma yadda za su wanke hannayen su.

Tuni dai aka kama mutane uku da ake zargi da hannu a kisan, ciki har da wani jimi'in ofishin diflomasiyyar Koriya ta Arewa, da wani ma'aikacin jirgin Arewar.

Labarai masu alaka