Bayar wa'adi da gwamnatin Niger ta yi ya kusa cika

Mahamadou Issoufou shugaban kasar Nijar
Wa'adin da gwamnatin kasar Nijar ta sanya wa masu hakar zinare na barin wuraren da suke hakar zinaren ya kusa cika.
Ganin hakan tuni wasu masu hakar zinaren da dama suka fara baro wuraren domin biyar doka kamar yadda suka furta.
Gwamnatin kasar dai, ta bayar da wa'adin 1 ga wata Maris, kan duk masu hakar zinare su bar wuraren.
Hukumomin na Nijar dai, sun bayar da dalilin cewa su na so su rufe wuraren da ake aikin zinaren na dan wani lokaci ,kuma ta hanane za su kawo tsarin da ya dace a cikin aikin hako zinaren a wannan wuri.
Tsarin da hukumomin su ka ce, za su kawo, shi ne zai sa 'yan kasar su rinka amfana da wuararen hakar zinaren yadda ya kamata.
A halin yanzu dai, cewar su bakine 'yan kasashen waje ke amfana da wuraren fiye da 'yan Nijar.