Dokar aure ba gudu ba ja da baya —Sarki Sanusi

Kano Emir Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sarki Muhammadu Sanusi na biyu ya ce nauyin zama uba ba yana nufin haifar 'ya'ya barkatai ba kula da su ba ne kawai

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, ya ce dokar da yake son bujuro da ita kan aure a jihar ba gudu babu ja da baya.

Sarkin wanda ya tabbatar da hakan, yayin jawabi a lokacin auren zawara 1500 da gwamnatin jihar Kanon ta gudanar, ranar Lahadi, ya ce, dokokin auren ne kawai za su taimaka wajen kawo karshen matsalolin da suka dabaibaye al'umma.

Sarki Sanusi ya kawo wani misali dangane da yadda marasa karfi kan yi aure su kuma hayayyafa ba tare da kula da yaran nasu ba.

"Wata mace ta kawo min karar mijinta cewa ya sake ta alhali suna da yara 10 tare saboda haka tana son a ja hankalin mijin nata wajen daukar nauyin yara guda bakwai, a inda ita kuma za ta kula da sauran ukun." In ji Sarki Sanusi.

Ya kara da cewa "sai na kirawo mijin na fada masa korafin tsohuwar matar tasa, a inda ya ce min ai yana da wata matar kuma suna da 'ya'ya takwas, ka ga ke nan yana da yara 18 shi kadai."

Sarki ya ce " ya tambayi sana'ar mutumin, a inda ya ce masa sana'arsa shushaina."

Wannan ne in ji Sarki Sanusi ya sa shi lasar takobin ganin an yi dokar da za ta taka wa irin wadannan halayyar burki.

Sai dai kuma sarkin ya nemi masu hannu da shuni masu mata daya da su kara, a inda gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya ce idan dai har mutum yana samun abin da yake so daga wurin matarsa, to babu dalilin karawa duk da yana da halin yin hakan.

Gwamnatin jihar Kano ne dai ta yi wa zawarawa 1500 daga kananan hukumomin jihar 44 aure, a inda ta biya sadakinsu naira 20,000 kowanne sannan kuma ta yi alkawarin yi musu kayan daki.

Da yake nasa jawabin, gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya ce nan gaba za a kara yi wa wasu mutum 1500 din irin wannan aure.