Zamu kare wuraren tarihi daga barnar IS- UNESCO

Iraq Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tun fiye da shekaru 3,300 aka kafa birnin Nimrud mai nisan kilomita 32 kudu da Mosul

Hukumar Raya Ilmi da Kimiya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO, ta ce barnar da mayaka na kungiyar IS suka yi ga wuraren tarihi a Iraqi ta fi yadda aka yi fargabar masu tayar da kayar bayan za su yi tun farko.

Shugabar hukumar ta UNESCO, Irina Bokova, ta ce hukumar na son kange wuraren tarihi da nufin kare su daga karin ta'adi na kungiyar IS.

Jami'an Iraqi sun ce suna ta samun dimbin kayakin tarihi da aka jibge a wasu ramuka da hanyoyin karkashin kasa a wasu sassa na Mosul da aka kwato daga 'yan gwagwarmaya a makwannin baya-bayan nan.

Gwamnati ta kuma yi kiyasin cewa kashi tamanin cikin dari na kufai dake birnin Nimrud mai cike da tarihi ne masu ikirarin jihadi suka lalata tun daga 2015