Faransa za ta tura dakarun soji Jamhuriyar Nijar

Gwamnatin Faransa ta ce za ta tura dakarun sojinta domin taimaka wa rundunar sojin Jamhuriyar Nijar, bayan da masu tayar da kayar baya suka yi kwanton-bauna ga wani ayarin sojojin Nijar dake sintiri suka kashe goma sha biyar daga cikin sojojin.

Matakin tura sojojin Faransar zuwa Nijar ya biyo bayan wata bukata ce daga shugaban Nijar din Muhammadou Issoufou, bayan harin wanda aka kai a ranar Laraba a kan iyakar kasar da Mali.

Ministan tsaro na Faransa, Jean-Yves Le Drian ne ya bayar da sanarwar matakin na tura sojojin kasar zuwa yankin na yammacin Afirka.

Sojojin wadanda ake jin adadinsu zai kama daga 50 zuwa 80, za su kasance cikin wata rundunar da dama ake da ita mai suna Rundunar Barkhane wacce ke yakar kungiyoyi masu ikirarin Jihadi a yankin Sahel.

Kasar Faransa dai ita ce ta yi wa jamhuriyar Nijar mulkin mallaka kuma kasashen biyu sun dade suna hada kai ta fuskar tsaro da tattalin arziki, galibi kuma Faransar ke taimaka wa Nijar din.