'Mayu' sun far wa Donald Trump

Trump
Bayanan hoto,

Trump ya gamu da kalubale iri-iri

Galibin abokan hamayyar shugaban Amurka Donald Trump sun yi imanin cewa dole su jira sai nan da shekaru hudu kafin burinsu na sauka daga shugabancin Amurka ya cika.

To sai dai mayu a Amurka na da kwarin gwiwar cewa ba sai an jira zuwa wannan lokacin ba.

Da tsakar daren Juma'a ne 'mayu' da mabiyansu a sassa daban-daban na Amurka suka yi wani taron tsinuwa da nufin kawar da shugaban kasar daga karagar mulki.

Wani shafin Facebook da aka kirkiro domin wannan sihirin, ya samu masoya sama da 10,500, kana aka kirkiro da maudu'in '#magicresistance' a shafin intanet.

Wannan al'amari dai ya fusata mabiya addinin kirista masu ra'ayin rikau wadanda suka zargi 'mayun' da shelar ''yakin sihiri''.

To sai dai wani marubuci, Micheal Hughes wanda ya bayyana kansa a matsayin 'mai ra'ayin siddabaru'' ya wallafa bayanan tsinuwar 'mayun' a shafin intanet, yana mai cewa ya ga irin wadannan bayanan da dama a shafukan 'mayu' na kashin kai.

''Taka ta kare''

Bayanan hoto,

Mayu sun tasam ma Trump

'Mayu' da ke cikin lamarin maitar na shirin yin tarukan tsinuwar a ranakun da wata (na sama) ya wuce rabi, har sai Mista Trump ya bar ofishin shugabancin Amurka.

An shirya yin taron sihirin na gaba a ranar 26 ga Maris., a inda aka bukaci su rika yin kulumboto kana su kona hoton Mista Trump da kyandir.

To sai dai wasu daga cikin magoya bayan Mista Trump na kokarin kare shi.

Kungiyar mabiya addinin kirista masu ra'ayin rikau da matukar kishin kasa wadda ake kira Christian Nationalist Alliance ta bayyana ranar 24 ga Faburairu, a matsayin ''ranar addu'o'i'' domin kalubalantar zumuntar mayun.

Kungiyar ta bayyana mayun a matsayin masu ikirarin ''sanin gaibu'', wadanda ke kokarin cin kuruwar Mista Trump, tana mai cewa zata bukaci jama'a su rika addu'o'i babu kakkautawa.

Mayun dai sun ce burinsu shi ne su makantar da Mista Trump domin kada ya iya aiwatar da 'miyagun manufofinsa'' don kada ya kawo rarrabuwar al'uma, da tauye 'yanci da cusa kiyayya a zukatan jama'a, da rudani da fargaba da kuma sanyin gwiwa.

Sun kuma ce za su yi kokarin daure harshen duk magoya bayan Trump su kasa yin magana.

A karkashin sharudan maita a Amurka, ba a 'makantarwa' da nufin cutar da mutumin da aka yi dominsa, illa domin hana shi cutar da sauran mutane. Masu ra'ayin maitar sun ce sun dauki matakin taka wa Trump birki ne domin jin dadin illahirin jama'a.

Mary Pat Azevedo wacce ta shiga taron maitar a Arizona, ta ce tana kallon lamarin a matsayin wani yunkuri na kawo ''hadin kai''. Ta shaida wa BBC cewa 'maye na kwarai ba zai taba sihirce mutum ba tare da yardarsa ba''. Ta kuma ce tana fatan ganin sauyi ta fuskar ruhi a Donald Trump da kuma siyasar Amurka.

Kawo yanzu dai shugaban na Amurka Donald Trump bai ce uffan ba kan yunkurin na mayu a Amurka.