An kama makamai a gidan tsohon gwamnan Benue

gabriel
Bayanan hoto,

Mista Suswan ya yi gwamnan jihar Binuwai daga 2007 zuwa 2015

Hukumar 'yan-sanda ciki ta DSS a Nijeriya ta bayyana cewa ta gano wasu makamai da suka hada da bindigogi da albarusai masu yawan gaske da kuma manyan motoci na alfarma a gidan tsohon gwamnan jihar Binuwai, Mista Gabriel Suswam dake Abuja babban birnin kasar.

Ko baya ga makamai, hukumar ta DSS ta ce an gano takardun filaye masu yawan gaske wadanda ake ci gaba da bincike game da su.

Hukumar ta 'yansandan ciki ta ce an bankado kayakin ne bayan wani bincike da jami'anta suka gudanar, kuma yanzu tsohon gwamnan yana hannunta tana yi masa tambayoyi, kamar yadda wata sanarwa daga wani jami'i na hukumar, Tony Opuiyo, ya raba wa manema labarai ta nuna.

Sanarwar ta kara da cewa ginin da aka gano kayakin na ciki yana kan titin Aguiyi Ironsi ke dake unguwar Maitama a Abuja.

Shi dai Mista Gabriel Suswam, ya yi mulkin jihar Binuwai dake yankin arewa ta tsakiyar kasar ne daga 2007 zuwa 2017.