Boko Haram: An kama 'yan Chadi a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Boko Haram kan yi barna a kasashen Nijeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kama wasu 'yan asalin kasar Chadi uku da ake zargin mayaka ne na kungiyar Boko Haram.

A wata sanarwa, rundunar ta ce ta kama mutanen da ake zargin ne a jihar Gombe a wani samame na hadin gwiwa tsakanin ta da jami'an tsaron farin kaya wato DDS.

Rundunar sojin Nigeria ta ce ta kama Bilal Muhammed Umar da Bashir Muhammed da kuma Muhammed Maigari Abubakar ne a unguwar Arawa da yankin Mallam Inna dake cikin birnin Gombe.

Sanarwar ta kara da cewa ana kyautata zaton wadanda aka kama, 'yan bangaren Albarnawi na kungiyar ta Boko Haram da ke aiki a Chadi da wasu yankuna na arewacin jihar Borno a Nijeriya.

A cewar sanarwar, mutanen sun je jihar Gombe da nufin aikata wani danyen aiki ne.