Ambaliyar ruwa a Chile ta janyo rashin ruwan sha

Yadda ruwan ke ambaliya
Bayanan hoto,

Miliyoyin 'yan kasar ne su ke tsananin bukatar taimakon ruwan sha

Ruwa mai karfin gaske da zaizayar kasar sun lalata babbar madatsar ruwan kasar Chile, lamarin da ya tilastawa hukumomi dakatar da tura ruwa ga al'uma kusan miliyan shida da ke yankunan babban birnin kasar Santiago.

Tuna ranar asabar ne aka fara sheka ruwan kamar da bakin kwarya mai hade da iska da guguwwa, wanda ya sanya kogin Maipo da birnin ya dogara da shi wajen samun tsaftataccen ruwan sha ya gurbata da tarkacen da guguwa ta kwaso daga birnin.

Firai ministan kasar Mariona Fernendez, ya ce kusan mutane miliyan shida ne ba su da tsaftataccen ruwan sha.

Yace a halin da ake ciki ana bukatar kai ruwa yankunann birnin Santiago, kuma akallah mutane kusan miliyan shida ne ke yankin da suke bukatar ruwa mai kyau.

Rashin ruwan sha shi ne babbar matsalar da ake fuskanta a Chile, ya yin da hukumomi suka bukaci masu gidajen cin abinci su rufe su.