Niger: Alkalai da gwamnati na musayar yawu kan cin hanci

Kasar jumhuriyar Nijar da sauren yankunanta
Bayanan hoto,

taswirar kasar jumhuriyar Nijar

Kungiyar alkalan kasa ta SAMAN a Jamhuriyar Niger ta bukaci ministan kudin na kasar da ya gabatar ma ta kwararan hujjojin akan zargin da ya yi.

Hassoumi Massaoudou ya yi zargin cewa, kamfanin Africard Ltd ya ba wasu alkalan kasar cin hanci a shari'ar da aka yi tsakanin kamfanin da gwamnatin Niger.

Kazalika kungiyar alkalan ta bukaci ministan kudin da ya yi murabus domin ya bayyana gaban kotu dangane da zargin almundahnar da ake yi masa ta kudade biliyan 200 na SEFA.

A game da wannan magana jam'iyar PNDS Tarayya mai mulki, ta ce hakan ba za ta samu ba.Ministan ba zai gurfana ba kuma bai zai aje aikin sa ba.

Shugaban jam'iyar ta PNDS Tarayya kuma Ministan harkokin cikin gida Bazoum Mohamed shi ya yi wannan furuci ,tare da cewa inda suna ha'inci da ba su nada 'yan 'yan wasu 'yan jam'iya ba a wasu wurare.

A halin yanzu dai ta na kasa a na dabo, tsakanin bangaren gwamnati da kuma kungiyar alkalan ta SAMAN.