An aurar da zawarawa sama da 1,500 a Kano

Wani bangare na auren zawarawa da aka yi a baya
Bayanan hoto,

A wani lokaci da ya gabata, gwamnati ta hada auren zawarawan da na samari da 'yan mata da suke bukatar tallafin kayan daki da sauran su

Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Nigeria ta aurar da zawarawa mata da maza sama da 1,500 a karshen mako.

Gwamnatin jihar ce ta dauki nauyi aurar da mutanen a wani yunkuri na ragewa iyayen da ba su da karfin aurar da 'ya'yan su hidima, da kuma rage yawan marasa aure a jihar.

Ba wannan ne karon farko da gwamnatin jihar Kano ta fara aurar da zawarawan ba, an faro wannan aikin ne tun zamanin tsohon gwamnan jihar wato Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso.

A wannan karo an zabo sama da mata da maza talatin a kowacce karamar hukuma da ke jihar, wanda kuma gwamnati ita ce ta biya kudin sadaki da kuma sanyan kayan daki ga ma'auraten.

An gudanar da dauren auren ne bayan da aka tantance ma'auraten ta bangaren lafiyar jikinsu da kuma hankalin su baki daya.

Wannan lamari dai na irin dauren wannan aure na sa matasa su natsu kuma ya kare su da yin zinace-zinace.

Masu saida kayan daki kamar su gado da kujeru dai na samun ciniki a lokuta irin wannan, wanda daya daga cikin manufar yin auren ita ce a bunkasa musu kasuwanci.