Adama Barrow ya kori babban hafsan sojin Gambia

Ousman Badjie

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ousman Badjie ya yi rantsuwar biyayya ga tsohon shugaban kasar, amma bai dauki mataki don hana kawar da shi ba

Shugaban kasar Gambiya, Adama Barrow, ya sallami babban hafsan sojin kasar, Janar Ousman Badjie.

Janar Badjie ya yi ranstuwar biyayya ga tsohon shugaban kasar, Yahya Jammeh, bayan zaben watan Disamba mai cike da cece-kuce.

Duk da hakan Janar Badjie ya shiga cikin masu rawa kan titunan kasar bayan Mista Barrow ya sha rantsuwar kama aiki a Senegal a watan Janairu.

Kuma a karkashinsa, rundunar sojin kasar ba ta nuna wata adawa ba a lokacin da sojojin kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta yamma, ECOWAS, suka kutsa kai Gambiya.

Sojojin yankin sun bayar da gudumawa wajen saka Mista Jammeh ya yarda da shan kaye, ya kuma bar kasar.

Rahotanni sun ce an maye gurbin Janar Badjie da magabacinsa, Janar Masanneh Kinteh.