Babu inda Musulunci ya ce ka doki matarka — Sarki Sunusi

Muhammadu Sunusi II
Bayanan hoto,

Muhammadu Sunusi ya ce ya shaida wa 'yarsa idan mijinta ya mare ta ta rama

Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sunusi na biyu ya yi gargadi ga masu dukan matansu, a inda ya ce ya shaida wa 'yarsa cewa idan mijinta ya mare ta to ta rama.

Sarki Sunusi ya ce babu inda addinin musulunci ya bai wa namiji damar dukan matarsa.

Sarki Sunusi ya kuma ja hankalin masu rike da sarautun gargajiya kan dukan matansu, a inda ya ce duk mai rawanin da aka samu da laifin dukan matarsa to a bakin rawaninsa.

Muhammdu Sunusi ya kara da cewa a tsarin sarautar Kano duk mai sarauta walau dai hakimi ko dagaci ko kuma mai unguwa har ma limami da aka kai fada yana dukan matarsa to zai ajiye rawaninsa.

Ku saurari jawabin na sarkin Kano da ya yi lokacin auren zawara 1,500 a Kano.

Bayanan sauti

Mari matarka ka rasa rawaninka — Sarki Sunusi