Garabasar da ke tattare da kafafen sadarwa na zamani

A ranar Litinin ne aka bude wani taro na mako guda a kan fasahar sadarwa ta zamani a Lagos, inda za a yi duba kan yadda matasa za su yi amfani da fasahar sadarwa ta zamani don iya dogaro da kansu. Muhammad Ibrahim Jega da Abdulganiyyu Rufai Yakubu, sun yi bayani kan yadda makyankasar kananan sana'o'i ke aiki.