Rikicin jagorancin jam'iyyar PDP bai kare ba

Har yanzu ricikin jam'iyar adawa ta PDP bai kare ba
Bayanan hoto,

Rikicin jam'iyar adawa ta PDP a Najeriya ya yi kamari

Dangantaka na kara yin tsami tsakanin bangarori biyu da ke jayayya a kan shugabancin babbar jam`iyyar adawa a Najeriya, wato PDP.

Bangaren Sanata Makarfi ya yi tir da matakin da Sanata Ali Madu Sherif ya dauka na bude hedikwatar jam'iyyar, bayan wani hukuncin da kotun daukaka kara a kasar ta yanke, har ma ya zargi jam'iyyar APC da rura wutar rikicin PDPn.

Jam'iyar APC ta musanta cewa tana da hannu a cikin rikicin cikin gidan jam'iyyar adawar.

Haka ma bangaren Ali Madu Sherif, shi ma ya musanta zargin banagaren na Makarfi.

Yanzu dai sai kutun koli kawai ce za ta iya yanke hukunci na karshe kan wannan danbarwar.

To amma kuma 'yan Najeriya da dama na tambayar kansu ko yaushe ne wannan rikici na jam'iyyar adawar zai kawo karshe?