Leicester ta doke Liverpool da ci 3-1.

Leicester ba ta yi kasa a gwiwa ba wannan karo
Bayanan hoto,

Leicester City ta yi nasara kan Liverpool

Leicester City ta yi tsallan badake ta fito daga rukunin masu faduwa daga gasar Premier bayan da a gidanta ta doke Liverpool da ci 3-1.

Wasan wanda shi ne na farko da ta yi bayan korar kocinta Claudio Ranieri, shi ne karon farko da ta yi nasara gasar ta Premier a wannan shekara ta 2017, kuma ya sa yanzu tana ta 15 a tebur da maki 24 a wasa 26.

Ita kuwa Liverpool tana matsayi na biyar da maki 49.

Vardy shi ya ci kwallayan na Leicester City guda biyu a mintuna na 28 da na 60, a yayin da Drinkwater ya ci tashi kwallon a minti na 39.