Trump: Za a karawa bangaren tsaro kudade

Donald Trump
Bayanan hoto,

Shugaba Trump ya ce zai kara kudaden da ake warewa ayyukan ababen more rayuwa, kamar tituna da kara tashoshin jirgin kasa, sai dai har yanzu bai tabo batun haraji ba

Shugaba Trump ya ce ya na son ganin karin kudaden da bangaren tsaron kasar ke kashewa a duk shekara da kashi 10 cikin 100 a kasafin kudin Amurka.

Shirin dai zai baiwa ma'aikatar tsaro ta Pentagon damar kashe sama da dala biliyan hamsin da hudu.

Za a samu karin kudin ne idan aka rage kudaden da ake fitarwa a kasafin kudi da suka shafi ayyukan sojin kasar, misali tallafi ga kasashen waje da kuma ayyukan kare muhalli.

Mista Trump ya ce za a karawa bangaren tsaro kudin ne saboda karfafa ayyukan da sojin Amurka ke yi, ta yadda babu wanda zai mu yadda kawowa kasar wargi ta fuskar tsaro.

Ya kara da cewa zai kara kudaden da ake warewa ayyukan ababen more rayuwa, kamar tituna da kara tashoshin jirgin kasa, sai dai har yanzu bai tabo batun haraji ba

A bangare guda kuma ma'aikatar tsaron kasar ta aikewa fadar White House shirinsu na kawo karshen kungiyar masu daga kayar baya ta Ism kamar yadda shugaba Trump din ya bukata tun da fari.