Ana bikin tunawa da kisan kiyashin da aka yi a Taiwan

Shugaba Tsai Ing-Wen ta Taiwan
Bayanan hoto,

Masu boren sun nuna adawa da yadda gwamnatin Kai-shek ke mulkin kasar, lamarin da ya sanya sojoji suka bude musu wuta

Al'umar kasar Taiwan su na bikin cika shekara 70 da kasar ta shiga wani mummunan yanayi da tarin kasar ba zai man ta da shi ba, aka yi wa lakabi kisan kiyashi ko 2-2-Massacre a turance.

A shekarar 1947, dakarun kasar karkashin shugaba Chiang Kai-shek mai mulki a wancan lokacin suka murkushe masu zanga-zangar adawa da gwamnati.

An yi kiyasin an kashe sama da dubu ashirin a lokacin zanga-zangar.

Shugaba mai mulki a yanzu, Tsai Ing-Wen wanda za ta gabatar da jawabi a wurin bikin tunawa da mamatan, ta yi alkawarin gabatar da wasu bayanai dangane da lamarin da ya faru.

Amma jam'iyyar adawa ta KMT wadda tsohon shugaba Kai-Shek da kasar China suka jagoranta, sun zargi shugabar da amfani da wannan dama dan yada manufofin siyasa, da yi wa jam'iyyar bita da kulli a wurin 'yan kasar.