Babu sabani tsakanin Buhari da Osinbajo - Gwamnati

Yemi Osinbajo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu masu sharhi na ganin Yemi Osinbajo na aiki tukuru tun bayan tafiyar Shugaba Buhari Ingila

Fadar shugaban Najeriya ta ce babu wani sabani tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da mukaddashinsa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Matakan da Osinbajo ya dauka na gaggawa wurin tunkarar matsalolin da kasar ke fuskanta tun bayan tafiyar Shugaba Buhari hutu, sun bai wa masu sharhi mamaki.

Kuma hakan ya sa wasu na ganin ya yi wa mai gidan nasa zarra a wata dayan da ya shafe yana lura da al'amuran kasar.

Sai dai fadar gwamnatin kasar ta ce duk wani yunkuri na nuna cewa Osinbajo ya fi Buhari "kokari ne na kawo rudani".

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu, ya ce 'yan adawa ne kawai suke son kawo rudu ta hanyar kimsa wa mutanen tunanin akwai rabuwar kai tsakanin shugaban da mataimakinsa.

Sanata Ojudu ya ce "Kusan a kullum sai [Osinbajo] ya tuntubi Shugaba BUhari saboda akwai abubuwan da ke bukatar hakan. Ina nufin yana neman shawararsa wajen zartar da manyan hukunce-hukunce."

Ya kuma kara da cewa irin ayyukan da Farfesa Osinbajo yake yi yana yi ne domin ya burge Shugaba Buhari ya kuma nuna masa cewa zai iya gudanar da al'amuran mulki ko da shugaban ba ya nan.

Tun dai ranar 19 ga watan Janairu Mista Osinbajo yake shugabancin Najeriya a matsayin mukaddashi sakamakon bulaguron da Shugaba Buhari ya yi zuwa Ingila domin ya huta sannan likitoci su duba lafiyarsa.

Daga lokacin kawo yanzu dai, mukaddashin shugaban ya zartar da wasu ayyuka da ake ganin sun kawo sauyi a kasar musamman ta fannin tattalin arziki.

A makon da ya gabata ne ya umarci babban bankin kasar, CBN da ya zuba miliyoyin daloli a kasuwar hada-hadar kudade, al'amarin kuma da ya sanya darajar Naira ta dan farfado.

A baya dai Shugaba Muhammadu Buhari ya hana yin hakan da manufar karfafa darajar kudin kasar.

Har wa yau shugaban ya yi hakan ne domin dakile shigo da kayayyaki daga kasashen waje wadanda ake ganin za a iya yinsu a cikin kasar.