Nigeria ta kwaso 'yan mata 41 daga Mali

Safarar mata domin aiki da karuwanci na karuwa
Bayanan hoto,

A 2016 an dawo da matan da aka yi safararsu 521

Gwamnatin Najeriya ta kama da kuma kwaso mata 'yan kasar 41 wadanda aka yi safarar su zuwa kasar Mali domin yin aikace-aikace da sunan neman kudi.

Rahotanni na cewa an kuma kama wasu mutane guda shida da ake zargi da safarar 'yan matan.

Jirgin sojin saman kasar ne dai ya sauke mutanen a filin jirgin Murtala Muhammad da ke Legas, da safiyar Litinin.

Mai ba wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin kasashen waje, Abike Debiri-Erewa ta ce " Shekarun 'yan matan ba su wuce 15 zuwa 17. Kuma sun yi tsammanin an kai su yin aiki ne amma daga bisani suka zama abin tausayi."

A nasa jawabin, mista Joseph Famakinwa, jami'in Hukumar Sanya ido kan safarar mutane na kudu maso yammacin Najeriya, ya ce a 2016 ma an dawo da mutanen da aka yi safarar su zuwa Malin 512.