Za a iya zartar wa wasu mata hukuncin kisa kan Kim Jong-nam

Koriya ta Arewa

Asalin hoton, REUTERS/AFP

Bayanan hoto,

Doan Thi Huong (dama) da Siti Aisyah (hagu) suka ce sun sammani suka wata wasan talibijin ne

Mai gabatar da kara na gwamnati, ya ce za a tuhumi wasu mata biyu da ake zargi da hannu a kisan dan'uwan shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-nam.

Babban mai Shari'a, Mohamed Apandi Ali, ya ce za a tuhumi matan wadanda suka fito daga Indonesia da Vietnam da laifin kuma idan an same su da laifin to za su iya fuskantar hukuncin kisa.

An dai ce matan sun shafa wa Kim Jong-nam wani magani mai dauke da sinadari mai guba a fuskarsa, a filin jirgin saman Malaysia a watan Fabrairu., a inda suka ce, sun yi zaton suna wani wasan talbijin ne.

Matan biyu dai Doan Thi huong, mai shekara 28 wadda 'yar Vietnam da Siti Aisyah, mai shekara 25 'yar Indonesia, na cikin mutane 10 da Malaysia ta gano na da hannu a kisan.