Faransa: Ana zargin wasu 'yan mata da alaka da IS

'Yan sandan kasar Faransa
Image caption Jami'an tsaro sun killace 'yan matan dan yi musu tambayoyi

An kama wasu 'yan mata hudu 'yan kasar Fransa, da ake zargin su na shirya aikata ta'addanci.

Kafar yada labaran Faransa ta ce 'yan matan na tsakanin shekara 14 ne da 18, kuma an kama su su na bin Rachid Kassim.

Wani dan kasar da ke cikin mayakan kungiyar IS, wanda kuma ya kware da baiwa mayakan horo kan dabarun yaki, su na musayar bayanai da 'yan matan ta kafar sadarwar internet.

Ko a farkon wannan watan jiragen yakin Amurka marasa matuka sun kusan kai hari maboyarsa.

Masu gabatar da kara sun ce 'yan matan sun tattauna kan yadda za su tada zaune tsaye, da haddasa fitina.

Kuma ta yi wu sun fara shirye-shiryen yin balaguro zuwa kasar Syria ko Iraqi wato kasashen da ake kallon su a matsayin cibiyar kungiyar ta IS.

Labarai masu alaka