Trump ya yi wa majalisa jawabi a karon farko

Image caption Bunkasa tattalin arzikin Amurka na cikin batutuwan da mista Trump ya fi maida hankali a kai.

A jawabi na farko da ya yiwa 'yan majalisar dokokin Amurka tun bayan shan rantsuwar kama aiki a watan da ya wuce, shugaba Trump ya yi alkawarin yin garanbawul ga manufofin kasar.

Ya ce lokaci ya yi da ya kamata Amurkawa su tabbatar da mafarkinsu, zai bukaci majalisa ta sanya hannu dan fitar da dala triliyan daya da za a zuba su baki daya a ayyukan more rayuwa.

Ta hakan ne za a samawa dubban 'yan kasar ayyukan yi, dan rage zaman kashe wando.

Haka kuma ayyukan ta'addanci da ake yi a kasar, da shigo da miyagun kwayoyi da ke illa ga rayuwar matasa ta iyakokin kasar shi ma ya zo karshe.

Yace sabon babin rayuwa ya bude ga 'yan kasar, sannan shekara da shekaru masu karamin karfi na shan wahala a kasar musamman ta fuskar haraji dan haka gwamnati na duba yuwuwar rage musu harajin.

Za dai a kara fadada binciken da ake yi dan tabbatar da wanda ya cancanci shiga Amurka, sannan mista Trump ya ce za ai wannan aiki ne tare da abokan huldarsu musamman ma dai na kasashen musulmi, da kuma hada karfi da karfe wajen yaki da kungiyar masu tada kayar baya ta IS.

Labarai masu alaka