Malaysia: An yaudari matan da suka kashe Kim Jong-nam

Matan a lokacin da za su shiga kotu
Image caption Duka matan biyu sun musanta zargin da ake musu

Masu shigar da kara na gwamnatin kasar Malaysia su na tuhumar matan nan biyu da aka kama tun da fari, da kisan dan uwan shugaban Koriya ta Arewa Kin Jong-un.

Ana zargin Siti Aisyah yar kasar Indonesia ce, sai kuma Doan Thi Houng 'yar kasar Vietnam da shafawa Kim Jong-nam wani mai a fuska da aka chakuda shi da guba mai saurin kisa a filin jirgin saman Malaysia Kuala Lampur a ranar 13 ga watan nan.

Hoton bidiyon kamarar CCTV shi ya nuna yadda matan biyu suka tunkari marigayin tare da shafa masa wani abu a fuska, masu shigar da kara sunce ta yiwu an yaudare su ne kan cewa ana shirya wani wasan kwaikwayo ne, sai daga baya suka gane ashe guba ce.

Harwayau, ana zargin wani jami'in dilomasiyya koriya ta arewa, da ma'aikacin jirgin arewar da kuma wani Ba'amurke da hannu a kisan, batun da arewa ta musanta.

Labarai masu alaka