Rasha da China sun hau kujerar naki

Kwarari masu bincike
Image caption Masu bincike na Majalasar Dinkin Duniya

Kasar Rasha da China ,sun hau kujerar naki a zauren Majalasar Dinkin Duniya game da maganar kada kuri'ar saka takunkuni ga Syria.

Amurika da Burtania da sauren kasashe, sun so a laddabtar da Syriar,game cewa ta yi amfani da makamai masu goba a cikin wani hari a yankin da 'yan tawaye suke.

Kadan ya yi saura kasashen da ke son a saka takunkumi kan kasar ta Syria su yi nasara, to sai dai kasashen biyu Rasha da China suka ki amincewa da yin hakan ta hanyar amfani da matsayin su na karfin fada da ita.

Wannan shi ne karo na bakoye da Rasha ke amfani da kujerarta wajen kawo kariya ga gwamnatin Bashar Al Assad daga fuskantar fusatar kasashen duniya .

Shugaba Putin na Rasha dai ya yi imanin da cewa, saka takunkomin ga kasar ta Syria ba shi da amfani ,kuma yin haka ba wata gwaninta ba ce.

A ganin shugaba Putin ,wannan na da hatsarin mai girma a yanzu ,domin ya na iya kawo watsewar tsarin tautaunawar sulhun samar da zaman lafiya da ake yi tsakanin gwamnatin kasar da kuma 'yan adawa a Geneva.

Amurika ta ce Rasha da China sune suka ki amincewa da akama dakarun kasar ta Syria kan laifin sakin gurbataciyar iskar guba da ta hallaka dinbin maza da mata da kuma yara kanana a yankin da yan tawaye masu adawa gwamnatin kasar ta Syria suke.