Nigeria: Kotu ta daure mawakin Hausa Sadiq Zazzabi

Sadiq Zazzabi Hakkin mallakar hoto Premium Times
Image caption Sadiq Zazzabi mawaki ne da ke goyon bayan tsohon gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso

Wata kotu a birnin Kanon Najeriya ta tura fitaccen mawakin Hausa Sadiq Zazzabi gidan kaso saboda wata sabuwar waka da ya fitar.

An gurfanar da mawakin ne a gaban hukumar tace fina-finai ta jihar saboda zargin sabawa dokar da ta ce wajibi ne duk sabuwar wakar da za a fitar sai an gabatar da ita ga hukumar.

Rahotanni sun ce Sadiq ya fitar da tasa wakar ce ba tare da amincewar hukumar ba.

Sai dai ya shaida wa jaridar Premium Times cewa an kama shi ne saboda yana goyon bayan tsohon gwamnan jihar Rabiu Musa Kwankwaso.

An dade ana samun takun-saka tsakanin Kwankwaso da kuma gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje.

Hukumar, wacce Ismaila Afakallahu ke jagoranta, ta ce duk da cewar mawakin ya gabatar da wakar gareta domin a bashi izinin wallafa wa, bai jira a bashi izinin ba kafin ya kaddamar da ita.

Labarai masu alaka