Nijar: Sace-sace sun addabi Damagaram

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana fama da matsalar kwararar baki daga birnin Agades mai makwabtaka da Damagaram

Hukumomi a jihar Damagaram ta Jamhuriyar Nijar sun koka kan yada sace-sace da ayyukan miyagun makamai ke ci gaba da zame musu manyan kalubale da ke ci musu tuwo a kwarya.

A kan haka ne ofishin magajin garin ya shirya wani zama na musamman da masu ruwa da tsaki kan sha'anin tsaro don gabatar da shawarwari kan yadda za a shawo kan wannan matsala.

Magajin birnin Dakta Bashir Sabo, ya ce wannan matsala ta sace-sace ta wuce duk yada ake zato, don haka dole a hada karfi da karfe don ganin an magance ta.

An shafe sa'o'i ana tattaunawa don gano bakin zaren warware matsalar, inda wasu daga cikin mahalarta taron suka zargi 'yan siyasa da cewa suna kara tunzura lamarin ta hanyar sa magoya bayansu su dinga ayyukan da ba su dace ba.

Ga dai rahoton da wakiliyar BBC a Nijar Tchima Illa Issoufou ta aiko:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Rahoto kan yawaitar sace-sace a Damagaram

Labarai masu alaka