Bera ya hana jirgi tashi a London

Jirgi Hakkin mallakar hoto Carly
Image caption An umarci fasinjoji su fita daga jirgin bayan da aka gano da bera a ciki

Wani jirgi da ya yi shirin tashi zuwa Amurka daga London ya kasa tashi daga filin jiragen sama na Heathrow, bayan da aka gano wani bera a cikinsa.

Fasinjojin da ke cikin jirgin wanda ya yi shirin tashi da misalin karfe 10:40 na safe agogon GMT, don zuwa birnin San Francisco sun zauna tsaf suna jiran jirgin ya ɗaga, sai kawai suka ji sanarwar faruwar lamarin, 'wanda ba a saba gani ba.'

Ma'aikatan jirgin sun shaida wa fasinjojin cewa jirgi ba zai iya tashi ba idan har akwai bera a cikinsa, don haka za a shirya musu tafiya a wani jirgin daban.

Daga karshe dai jirgin ya tashi bayan sa'o'i hudu.

Wata fasinja mai suna Carly, ta ce, 'A lokacin da aka yi sanarwar, sai da yawan fasinjojin suka ƙi yarda da batun.'

Ta ce, "Bani da tabbas kan yadda lamarin ya zo wa mutane."

'Basirar yin fim'

Ta ce an shaida musu su cewa an samo musu wani jirgin daban, amma dai fasinjojin sun yi jiran sa'o'i da yawa don a bude musu wata kofar kafin su samu damar tashi.

Wasu daga cikin fasinjojin sun bayyana yadda suka ji da faruwar lamarin a shafinsu na Twitter.

Matt Watt ya rubuta cewawrote: "Yanzu aka soke tashin jirgin da na hau don zuwa San Francisco saboda bera ya shiga cikin jirgin. To bai samu bisa ba ne?? #britishairways", yayin da shi kuwa @midlandsound A Haiku, ya rubuta cewa: "Muna dab da tashi zuwa San Francisco, amma akwai bera a jirgin, dole mu sauka dukkan mu.

Ya sake rubuta: "Zan sayarwa masu shirya fim wannan labarin. Zai iya kama da wani fim da aka taba shiryawa na yadda aka ga maciji a cikin jirgi."

Hakkin mallakar hoto Rebecca Cafe

Kamfanin jiragen sama na British Airways ya ce, "Mun san kowa a cikin jirgin nan na son bin mu zuwa San Francisco, amma a wannan tafiyar akwai wani dan karamin fasinja da dole sai mun sauke shi ya kama gabansa.

"A yanzu haka duk wata halitta mai kafa biyu (dan adam) da ke cikin jirgin nan, za su kama hanyar California, a yi mana afuwa sakamakon bata lokacin da muka yi."

Hukumar filin jiragen sama ta Heathrow, ta ce ba za ta ce komai ba kan abin da ya shafi wani kamfanin jirage.

A shekarar 2015 ma an soke tashin jirgin da wani dan wasan dambe David Haye, ke ciki, saboda ganin bera da aka yi a cikinsa.

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba