'Ziyarar Sarkin Saudiyya zuwa Indonesia na cike da fariya'

king salman Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Images

Sarkin Saudiyya ya ziyarci kasar Indonesiya a karon farko da wani Sarki na kasar ya yi irin ta cikin shekaru 47.

A yayin da ziyarar tasa, wadda ta kasuwanci ce zuwa kasar da ta fi ko wacce yawan Musulmai a duniya ke daukar hankali, haka ma dan hutun da zai yi a tsibirin Bali, da irin kayan alatun da zai tafi da su ke kara daukar hankalin jama'a.

Sarki Salman dan Abdul Aziz al-Saud ya isa birnin Jakarta tun ranar Laraba, a wani bangare na wata ziyara da yake yi ta tsawon wata guda a wasu kasashen yankin Asiya, da suka hada da Malesiya, da Brunei, da Japan, da China da kuma Maldives.

Wakilin BBC a Indonesiya Christine Franciska, ya yi duba kan yadda mutanen kasar suke ta sha'awar ziyarar sarkin.

'Motocin alfarmada tawaga ta kasaita'

Kafofin yada labarai na Indonesiya sun bayar da rahoton cewa sarkin ya taho da kayayyakin da nauyinsu ya kai ton 459, wadanda suka hada da motoci kirar mercedes-Benz S600s guda biyu, da kuma lifta mai aiki da lantarki guda biyu.

Wani kamfanin jirage da aka dora wa alhakin dakon kayayyakin sarkin mai suna"Jasa Angkasa Semesta" ya shaida wa kafar yada labarai ta Antara cewa an sauke ton 63 na kayan a Jakarta, yayin da za a kai sauran ton 396 na kayan tsibirin Bali.

Tawagar tasa ta hada da mutum 620 'yan rakiya, da wakilai 800 wadanda suka hada da ministoci 10 da kuma 'ya'yan sarki 25.

Kamfanin ya kara da cewa jirage 27 ne za su yi jigilar tawagar sarkin zuwa birnin Jakarta, sannan kuma jirage tara su dauke su zuwa tsibirin Bali.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sarkin ya je da motoci kirar Mercedes guda biyu

Duk da cewa dai an san Sarakuna da shugabannin kasashe sun saba tafiye-tafiye da kayayyakin alatu tare da babbar tawaga, to amma mutanen Indonesiya na ganin alfahari ya yi yawa a wannan ziyarar.

Wani mai amfani da shafin Twitter ya rubuta cewa, "Da yawan 'yan Indonesiya suna ganin cewar sarkin Saudiyya ya nuna fariya sosai a wannan tafiya. Ni dai na fi alfahari da shugaban kasarmu Jokowi saboda saukin kansa."

Sarakunan Saudiyya ba su cika kai ziyara ba

Rabon da wani sarkin Saudiyya ya ziyarci kasar Indonesiya tun a shekarar 1970, lokacin da sarki Faisal bin Abdul-Aziz ya ziyarci shugaba Suharto a Jakarta.

Ziyarar Sarki Salman na zuwa ne shekara biyu bayan shugaba Widodo ya ziyarci kasar Saudiyya domin tallata zuba jari a kasar tasa.

A makon da ya gabata ne sakataren ministocin kasar Indonesiya, Pramono Anung, ya shaida wa manema labarai cewa, "Wannan ziyara ce ta abokan juna na kut-da-kut, tsakanin kasashe biyu"

Hakkin mallakar hoto TWITTER
Image caption "Sarki Salman tare da Firai ministan Malesiya

Sarkin ya fara ziyarar tasa ne zuwa kasashen yankin ranar a Litinin inda ya fara da kasar Malesiya, kasar da wanda ya gada ya ziyarta a shekarar 2006, inda suka tattauna al'amuran da suka shafi diflomasiyya tare da Firai minista Najib AbdulRazak

Ziyara ce mai gwabi

Gwamnati kasar ta Indonesiya ta ce kasar za ta amfana daga wannan ziyara, saboda Saudiyya za ta zuba jari na kimanin dala biliyan 25. Yarjejeniyoyin da za a kulla sun hada da zuba jarin dala biliyan shida da kamfanin mai na "Aramco" da ke Saudiyya zai yia Indonesiya.

Ko a ranar Talata ma dai kamfanin man na Aramco ya kulla yarjejeniyar zuba jarin da ya kai dala biliyan bakwai a kamfanin mai na Malesiya.

Haka kuma ana sa ran cewa ziyarar shakatawa da Sarkin zai kai tsibirin Bali za ta kara inganta harkokin yawon shakatawar kasar.

Wani mai lura da al'amuran gabas-ta-tsakiya kuma mamba a kungiyar malamai ta Indonesiya, Zuhairi Misrawi, ya shaida wa BBC cewa, "Ziyarar ta musamman ce a bangaren kasar Indonesiya."

Ya kara da cewa, "Za su tattauna muhimman al'amura da suka shafi tattalin arziki, da al'adu, da kuma yawon shakatawa. Abin da muke son gani yanzu shi ne Saudiyya ta cika alkawuran da ta daukawa kasarmu na zuba jari."

Cude ni-in-cude-ka

A yayin da ziyarar za ta yi wa Indonesiya amfani sosai ta fannin tattalin arziki, masu sharhi na ganin ita ma Saudiyyar za ta ci moriyar abin.

Ta bangare dabarun zuba jari, wanda zai taimaka wa kasar rage dogaro a kan man fetur, Saudiyar dai ta fara karkata kan aikin hajji wanda shi ne na biyu wajen kawo wa kasar kudaden shiga bayan man fetur.

Hakkin mallakar hoto AFP PHOTO / ADEK BERRY
Image caption kasar Indonesiya ita ce kasar da tafi ko wace kasa yawan mahajjata

Zuhairi Miswari ya kara da cewa, "Kasar Indonesiya dai ta kasance kasar da tafi kawo wa Saudiya kudin shiga a duk lokacin aikin Hajji da kuma Umara."

"Duk da cewa Saudiyya ta kara yawan kudin bizar da mahajjata ke biya, bana tunanin hakan zai rage yawan mahajjatan da ke zuwa daga kasar Indonesiya," inji Zuhairi

Sai dai wasu 'yan Indonesiyan na nuna damuwarsu kan karin kudin aikin Hajjin da Saudiyyar ta yi.

Mista Misrawi ya kara da cewa, "Ta bangaren Indonesiya ya kamata mu kula da shirinsu na rage yawan mahajjata, saboda abin da mu muka dauka tsaka-tsaki, su a wajensu ba haka abin yake ba."

"Ya kamata gwamnatin Indonesiya ta gane haka. Muna so su jajirce su cewa Saudiyya kada su shiga cikin akidunmu."

Labarai masu alaka

Karin bayani