India: 'Da ruwan rafi ake Coca-Cola da Pepsi'

Indiya Coca-cola, Pepsi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu fafutuka a wasu sassan Indiya sun yi ta kira kan a haramta yin Pepsi da Coca Cola

Wata kotu da ke Kudancin Indiya ta yanke hukunci cewa kamfanonin da suke sarrafa Coca-cola da Pepsi 'mai yiwuwa' suna amfani ne da ruwan rafi, duk da kokarin da abokan gasarsu ke yi na hanasu.

Watanni hudu da suka gabata ne aka sanya wata doka ta wucin gadi da ta hana su samun damar diban ruwa daga kogin Tamirabarani da ke garin Tamil Nadu, bayan da wata kungiyar masu sayen kayan amfanin yau da kullum ta yankin, suka kalubalanci cewa yawan diban ruwan kogin da suke yi na kawo cikasa ga harkar noma ga Manoman yankin.

Sai dai kamfanonin sun ce ba a yi musu adalci ba a wannan lamari.

An hana sayar da Coca-Cola a India

A ranar Laraba ne wasu masu shaguna a garin Tamil Nadu suka fara daina sayae Coca-colan da Pepsi, kamar yadda kungiyar 'yan kasuwa ta tsara.

Labarai masu alaka