An hana ladabtar da yara da duka a Zimbabwe

Zimbabwe Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukuncin zai hana ladabtar da yara da duka a makarantun kasar Zimbabawe in har kotun tsarin mulki ta amince

Wata babbar kotun Zimbawe ta hana ladabtar da yara da duka a gida da makaranta.

Shari'ar da ake ganin za ta sauya yadda ake tarbiyyar yara a kasar, ta zo ne bayan wani malami ya doki wata daliba 'yar aji daya a makarantar firamare, domin ba ta bari an rattaba hannu kan aikin da aka bata ta yi a gida ba.

Uwar yarinyar ta kai kara kotun ne bayan ta ce ta ga ciwon da yarinyar ta ji sanadiyyar dukan.

Ta ce ladabtarwa da duka babban tashin hankali ne da kuma rashin tausayi.

Kuma wata babbar kotun kasar ta yarda da hakan.

Wasu iyaye na sukar hukuncin da kotun ta yanke a daidai lokacin da wasu kungiyoyi masu fafatuka ke cewar ya kamata a samu irin wannan hukuncin tun tuni.

Amma dai sai kotun tsarin mulki ta tabbatar da hukuncin kafin a fara amfani da shi.