Asibiti ya rufta kan majinyata a Afirka ta Kudu

South Africa Hakkin mallakar hoto News24
Image caption Kafar News 24 ta ce an ceci mutum daya daga baraguzan.

Rahotanni sun ce majinyata sun makale bayan da wani bangare na rufin ginin asibitin da suke ciki a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu ya rufta.

Asibitin Charlotte Maxeke daya ne daga cikin asibitocin gwamnatin da suka fi samun mutane a brinin inda daruruwan mutane ke zuwa a ko wacce rana.

Ba a tabbatar da ko mutuane nawa ne suka ji rauni ba tukunna, amma masu aikin ceto sun ce zuwa yanzu an mutum hudu da suka ji rauni na karbar taimakon gaggawa.

Masu aikin kiwon lafiya na jiran ko ta kwana a lokacin da ma'aikata ke ta kokarin tona baraguzan ginin.

Wani mai magana da yawun bakin hukumar bayar da agajin gaggawa, ya shaidawa kafar yada labari ta News24, cewar mutum shida sun makale cikin baraguzan a lokacin da suka isa wurin.

An yi imanin cewar an riga an fitar da wasu mutane daga karkashin baraguzan ginin.

Labarai masu alaka