Maganin zazzabi mai tasiri kan cutukan jima'i

Malaria Hakkin mallakar hoto UN/Martine Perret
Image caption An samu sabuwar hujjar da ke nuna cewar maganin zazzabin cizon sauro yana maganin cutukan da ake samu ta hanyar jima'i.

Nigeria: Mutane dubu 250 ke kamuwa da kansa a shekara

Wani magani da aka bai wa mata masu juna biyu a kasashe 35 domin kare su daga kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro, an gano kuma cewa yana ba da kariya ga cutukan da ake iya dauka a wajen jima'i.

Binciken ya ce maganin ka iya yin tasiri kan cuta biyu da ke da hatsari ga mata masu juna biyu da jariranSU.

Makarantar nazarin tsafta da ilimin magungunan kasashe masu zafi (London School of Hygiene & Tropical Medicine) ta ce baya ga kare matan daga zazzabin cizon sauro, maganin mai suna sulphadoxine-pyrimethamine (SP) na kuma ba da kariya kan cutukan da ake dauka ta hanyar jima'i, kamarsu gonorrhoea da chlamydia da trichomoniasis da kuma bacterial vaginosis.

A duk shekara ana haihuwar jarirai dubu 880 ba rai da kuma wasu jarirai miliyan 1.2 da ke mutuwa a lokacin da aka haife su a Afirka ta kudu da Sahara.

Ana kuma danganta akasarin mace-macen da cutukan da mata masu juna biyu ke samu a lokacin da suke dauke da juna biyu.

Marubutan sun ce suna fata, binciken zai sanya kara kaimi wajen bai wa mata masu juna biyu, da ke lardunan da cutar zazzabin cizon sauro ya fi kamari kulawa.