Jami'an tsaro na binciken ba-sani-ba-sabo a Nijar

Jami'an tsaron sun kama mutane da dama da mugayen kwayoyi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jami'an tsaron sun kama mutane da dama da mugayen kwayoyi

A Jamhuriyar Nijar jami'an tsaro ne daga hukumar Kwastam har ya zuwa 'yan sanda, suke gudanar da binciken ba sani ba sabo ga duk wata motar da ke kokarin shiga wani gari daga wani garin.

Ta hakan ne dai ake samun makamai irin su bindigogi da harsasai daga wasu matafiya, sannan kuma ana samun masu safarar miyagun kwayoyi.

Jami'an tsaron sun kama mutum uku dauke da tabar wiwi da kuma fasfo 23 na wasu kasashe a garin Gidan Roumdji na jihar Maradi.

Ko ma dai a garin Maradin 'yan sanda sun kai samame gidan wani mutum da misalin karfe biya na subahin ranar Laraba, inda nan ma suka samo wiwi da dama.

Daga Damagaram wakiliyamu Tchima Illa Issoufou na da cigaban wannan batu.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Rahoto kan binciken custom a Nijar

Labarai masu alaka