Ka san tsananin da ya sa jaki ɗaukar raƙumi?

Somalia drought Hakkin mallakar hoto @Mukhtary
Image caption Rashin abinci ya sa kasar ta dukufa wajen neman tallafi don magance wannan annoba

'Yan Somaliya kimanin miliyan uku ne ke fuskantar matsananciyar yunwa sakamakon wani mummunan fari da ba a taɓa ganin irinsa ba cikin shekaru gommai a ƙasar.

Tsawon shekaru uku kenan, Somalia ba ta samu damuna mai albarka ba.

A wani mummunan fari da aka yi a ƙasar shekara biyar da ta gabata, sama da mutum dubu 250 ne suka mutu.

Farin dai a wannan shekara ya fi shafar yankin arewa maso gabashin ƙasar da kuma kudancin Somalia ne.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tun bayan hawansa kan mulki, shugaba Abdullahi Farmajo ya nemi kasashe su taimaka wa Somalia

Wani ma'aikacin agaji ya wallafa wasu hotuna a shafin Tweeter inda yake nuna tsananin tasirin da fari ya yi a ƙasar.

Ɗaya daga cikin hotunan ya nuna jakuna na jan wata amalanke ɗauke da raƙumi daga wani yankin mai fama da fari.

Ma'aikacin agajin Mukhtar Mohammed ya ce wannan wani fari ne da ba a ga kamarsa ba, cikin lardin El-Barde na yankin Bakool.

Bayan rantsar da shi a watan jiya, sabon shugaban Somalia, Mohamed Abdullahi Farmajo, ya yi kira ga 'yan Somalia mazauna ƙasashen ƙetare da su tallafa wa al'ummar ƙasar.

Labarai masu alaka