Babban lauyan Amurka ya tsame hannu a bincike kan Rasha

Jeff Sessions
Image caption Jeff Sessions ya ce a matsayinsa na sanata ya zanta da jakadan Rasha

Babban lauyan Amurka, Jeff Sessions ya tsame hannunsa daga binciken da hukumar FBI ke gudanarwa game da zargin katsalandan ɗin Rasha a zaɓen ƙasar.

'Yan jam'iyyar adawa ta Dimokrat sun buƙaci ya sauka daga kan muƙaminsa lokacin da ta bayyana cewa ya gana da jakadan Rasha yayin yaƙin neman zaɓen shugaban Amurka.

Babban lauyan gwamnatin ya ba da tabbaci a yayin zaman sauraren tabbatar da naɗinsa a watan Janairu cewa bai yi wata "hulɗar sadarwa da Rashawa ba".

A cikin wata sanarwa Jeff Sessions ya ce "Na yanke shawarar tsame kaina daga duk wani bincike yanzu ko a nan gaba kan duk wani batu ta kowacce siga da yaƙin neman zaɓen shugaban Amurka."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan jam'iyyar Dimokrat dai sun ce Jeff Sessions ya sauka daga muƙaminsa

"Na ji daɗi cewa wasu sun ɗauki ra'ayin cewa wannan bayani ƙarya ne. Abin da ake zargina da shi ba manufata ba ce. Kuma hakan ba daidai ba ne."

Me ake zargin Mr Sessions da aikatawa?

A lokacin zaman sauraren majalisar dattijai ranar 10 ga watan Janairu, an tambayi Mr Sessions: "Idan aka samu wata shaida cewa wani da ke da alaƙa da yaƙin neman zaɓen Trump ya tattauna da gwamnatin Rasha, a lokacin fafutukar neman zaɓe, me za ka yi?"

Jeff Sessions ya mayar da martanin cewa: "Ba ni da wata masaniya kan waɗannan abubuwa. An kira ni, na yi wakilci sau ɗaya ko sau biyu a lokacin yaƙin neman zaɓe amma ban yi wata tattaunawa da Rashawa ba."

Sai dai a yanzu ta bayyana Mr Sessions da jakadan Rasha a Amurka, Sergei Kislyak, sun yi wata tattaunawar sirri a ofishin Sessions cikin watan Satumba, ya kuma zanta tun farko a wani taro da sauran wasu jakadu da dama.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Donald Trump dai ya ce yana da cikakken ƙwarin gwiwa a kan Atoni Janar ɗin

Tsohon sanatan Alabaman ya yi taruka da jakadun ƙasashen waje sama da 25 a bara.

Yayin wani taron manema labarai a ranar Alhamis, Mista Sessions ya ce ya zanta da jakadan Rasha a matsayinsa na sanatan Amurka amma ba wakilin Donald Trump ba.

Ya ce a lokacin hirarsu da jakadan Rasha, ya faɗa masa cewa ya taɓa zuwa Rasha a wani ayarin wani coci cikin 1991.

Ko ana iya tuhumarsa da yin ƙarya?

Sai dai masu gabatar da ƙara sun nuna cewa ba kawai bayanan ƙarya Jeff Sessions ya bayar ba, da gangan ya kuma yi wasa da hankalin wakilan kwamitin majalisar dattijan Amurka a kan wannan al'amari.

Ya dai nanata a ranar Alhamis cewa ya bayar da amsa ce daidai da tambayar da aka yi masa, wadda ya jaddada cewa ya yi imani an yi ta ne a kan hulɗar da ta shafi yaƙin neman zaɓe amma ba kan batun hirarsa a matsayin sanata ba.

Labarai masu alaka