Masanan kimiyya sun yi wa wani matashi 'maganin sikila'

Red cells Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Jajayen ƙwayoyin jini a kewaye siffarsu take amma rashin lafiya sai ta sanya su komawa nukus

Masana kimiyya sun ce sun ƙirƙiro wata sabuwar hanyar warkar da mutane masu fama da matsananciyar larurar nan ta jini wato amosanin jini ko kuma sikila.

Miliyoyin mutane ne akasari a nahiyar Afirka suke fama da irin wannan cuta a faɗin duniya.

Karon farko, masana kimiyya sun yi amfani da hanyar maye ƙwayayen halittun gado marasa lafiya a cikin ƙwayoyin halitta na wani matashin Bafaranshe, wanda kuma suka ce a yanzu ya rabu da dukkan alamomin wannan cuta da kuma ciwon da take haddasawa.

Cutar sikila takan janyo lafiyayyiyar ƙwayar jini ta yi nukus, lamarin da ke toshe zagayawar jini zuwa sassan jiki da kuma haddasa matsalolin lafiya masu tsanani ciki har da shanyewar sashen jiki.

Cutar dai ta fi ƙamari ne a Afirka amma takan shafi sauran mutane a wasu yankuna na duniya.

Wakilin BBC ya ce "masanan suna taka tsantsan wajen yin amfani da kalmar waraka, saboda maras lafiya ɗaya ne aka yi wa magani ta wannan hanya.

Amma dai binciken ya nuna ƙarfin da wannan salon magani yake da shi wajen sauya rayuwar masu fama da cutar sikila"

Labarai masu alaka