Shin ya kamata a sanya ido kan shafukan sada zumunta?

Wasu mahalarta taron shafukan sada zumunta a Lagos
Image caption Wasu mahalarta taron shafukan sada zumunta a Lagos

Batun sanya ido kan yadda ake amfani da shafukan sada zumunta na zamani a Najeriya al'amari ne da ke saurin tayar da jijiyoyin wuya, saboda yadda aka samu sabanin fahimta a kansa.

'Yan kasar da dama na ganin sanya ido kan shafukan na sada zumunta wani yunkuri ne na danne hakkin da kundin tsarin mulki ya ba su ta fadar albarkacin bakinsu, yayin da masu son a kayyade yadda ake amfani da shafukan ke cewa barin su su ci karensu babu babbaka zai haifar da gagarumar illa ga kasar.

Hakan ne ma ya sa a watan Disambar shekarar 2015, lokacin da majalisar dattawan kasar ta so kawo dokar da za ta sanya ido kan masu amfani da shafukan, aka yi ta kai ruwa rana tsakanin masu fafutika da wasu 'yan majalisar.

Da a ce an zartar da kudirin dokar, da ya bayar da dama an soma daure, masu mu'amala da shafukan sada zumuntar da suka yi wa wani "kazafi" tsawon shekara biyu a gidan yari.

Dan majalisar ya da gabatar da kurin, Bala Ibn Na'Allah, ya ce bai kamata a rika barin 'yan kasar suna cin zarafin mutane musamman a shafukan sada zumunta ba.

A cewarsa, babu wata kasa a duniya da za ta yarda 'ya'yanta su rika rubuce-rubuce da ke "yin zarge-zarge na babu gaira babu dalili" ba tare da an hukunta su ba.

Kudurin dokar ya bukaci "A yi daurin shekara bakwai ko tarar N5m ga duk mutumin da -- da gangan -- ya watsa labaran karya wadanda za su iya yin barazana ga tsaron kasa ko kuma labaran da za su sa 'yan kasa su yi wa gwamnati tawaye".

'Yan Kannywood na baje-koli a shafukan zumunta

'Yawan amfani da shafukan zumunta yana sanya ƙyashi'

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A lokuta da dama kafofin sada zumunta suna taka rawa wajen matsawa hukumomi lamba don su aiwatar da wasu abubuwan

Haka kuma kudurin ya nemi "A yi daurin shekara biyu ko sanya tarar N2m kan duk wanda ya yi amfani da sakon tes da Twitter da WhatsApp, da ma sauran shafukan sada zumunta wajen yin zage-zage da zummar harzuka mutane".

Sai dai shugaban majalisar datttawan Sanata Bukola Saraki, da ma shugaban kasar Muhammadu Buhari, sun nuna rashin amincewarsu ga kudirin dokar, lamarin da ya sa ala tilas aka yi watsi da shi.

Bambancin ra'ayi

Amma a tattaunawar da na yi da wasu mahalarta taro kan shafukan intanet da na sada zumunta da ake yi shekara-shekara a Lagos da ke kudu maso yammacin Najeriya, sun sake tasowa da batun, ko da yake su ma suna da mabambantan ra'ayi a kansa.

Bishop Chitumu, wani mai yawan mu'amala da shafin Twitter, ya shaida min cewa dole a kayyade yadda ake amfani da wadannan shafukan Idan ba haka ba za a ci gaba da fuskantar matsalolin kyamar juna da tashe-tashen hankula da makamantansu.

A cewarsa, "Tun da aka yi watsi da kudirin dokar da ya so sanya ido kan wadannan shafuka al'amura sai dada rikicewa suke yi."

Ya kara da cewa, "Mutane na yin amfani da su wajen cin zarafin juna da kage da tayar da rikici. Ka dubi yadda wasu suka rika aike wa da sakonnin karya a game da rikicin Kudancin Kaduna".

Mista Chitumu ya kara da cewa ya kamata Najeriya ta dauki mataki irin na kasashe kamar China domin sanya idanu kan wadannan shafukan sada zumunta, yana mai cewa hakan ne kawai zai sa mutane su shiga taitayinsu.

Sai dai Bobbi Ibrahim, ya shaida min cewa babu yadda sanya ido kan shafukan na sada zumunta zai magance matsalolin labaran kanzon-kurege da kuma kyamar da mutane ke yi wa juna a Najeriya.

Ya kara da cewa, "Wadannan 'yan siyasa da ke son hana mu fadin albarkacin bakinmu su ne suka yi amfani da shafukan wurin cin zabe, kuma suna jin tsoro ne kada mu rika tambayar su bisa alkawuran da suka dauka."

Bobbi Ibrahim ya ci gaba da cewa, "Ya kamata ka sani cewa idan ina kyamar ka -- ko ana amfani da shafukan sada zumunta ko ba a yi -- zan ci gaba da nuna maka kiyayya ko kuma na rika tayar da rikici. Don haka bai kamata a rika dora musu laifi ba".

Rahama Sadau ta fara fitowa a waka salon hip hop

Mr Ibrahim ya ce abubuwan da suka kamata a yi su ne a hana kananan yara amfani da shafukan intanet domin barin su yana hana su karatu sannan zai bata tabiyyar da ake yi musu.

Yaɗa baɗala

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana amfani da shafin Instagram wajen wallafa hotuna da bidiyo

Baya ga batun cewa ana cin zarafin mutane a shafukan sada zumunta da muhawara a Najeriya, akwai kuma wani al'amari da shi ma yake ci wa wasu 'yan kasar tuwo a kwarya, na yadda matasa musamman mata ke wallafa hotunan 'yan mata kala-kala mai nuna kusan tsiraicinsu a shafukan.

Mafi yawan waɗannan 'yanmata sun fi amfani da shafin Instagram ne wajen aikata wannan abu, kuma sau da yawa za a samu cewa dubban mutane na bin irin waɗannan shafukan.

Sheriff Almuhajir wani ma'abocin amfani da kafofin sadarwa na zamani ne, kuma a ganinsa, "Al-ummah ce ta karkata wajen son ganin tsiraicin mata da kuma mayar da tsiraicin wani ma'auni na tantance kyau. Su kuma mata dama Allah ya saka ma su son kyau da son samun yabon mutane."

"Sai bukatun suka hadu da zamanin da ya kawo wata kafa ta sadarwa da ke taimaka yada hakan, shi ne kowa ya karba," inji Almuhajir.

'Yan kasar da dama dai na ganin akwai bukatar sanya ido kan kafofin sadarwar ta wannan bangare na hana yaɗuwar baɗala, don kare tarbiyyar matasa da yara masu tasowa, da ma kare martabar addini da al'ada.

Kun san abin da dalolin Andrew yakubu za su iya yi a Nigeria?