'Muna fafutukar tabbatar da samun sabuwar Nigeria'

Nigerian Flag Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyar ta ce Najeriya tana da yawan arzikin da bai kamata a ce 'yan kasar na shan wahala ba

A Nigeria, wata kungiya mai suna National Rebirth Group da ta ce tana fafutukar tabbatar da sabuwar Nigeria, ta koka a kan mawuyacin hali da talakawan kasar ke ciki.

Kungiyar wadda ta ce burinta shi ne sauya salon gudanar da shugabanci a Najeriya, ta bayyana takaici kan yadda gwamnatocin baya da na yanzu, ke tafiyar da al'amuran da suka shafi rayuwar 'yan kasa.

Alhaji Salisu Mohammed, shi ne shugaban kungiyar, ya kuma shaida wa BBC cewa, wajibi ne a dauki matakai na sauya yadda al'amura ke gudana a Najeriya.

"Dole mu yi wa kanmu wani abu saboda abubuwa na rashin jin dadi da ke faruwa a kasar nan, musamman idan aka duba yadda yunwa take kara yawa, a halin yanzu ba talakawa ba har wasu masu rufin asirin ma ba sa iya ciyar da kansu da wadanda ke karkashinsu," inji Alhaji Mohammed.

Ya kara da cewa hakan na faruwa ne saboda an fito da wasu hanyoyi da ba su da makoma ta alheri na yadda za a inganta abubuwa.

Rashin gamsuwa

Duk da cewa gwamnatocin da suka shude da na yanzu sun ta yin alkawuran inganta al'amura, Alhaji Mohammed ya ce su ba su gamsu ba, don ba su gani a kasa ba.

Ya ce dukkan gwamnatocin ba su kawo matakan da za su gamsar da 'yan kasa ba, "A yanzu haka fa kusan kashi 70 cikin 100 na al'umar kasar nan sun rufta cikin talauci."

Ga dai yadda cikakkiyar hirar tasu ta kasance da Yusuf Tijjani:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hira da kungiyar da ke son samar da sabuwar Najeriya

Hauhawar farashi: 'Yan Nigeria na ɗanɗana kuɗarsu

An shafe shekaru da dama Najeriya na fama da matsaloli da suka shafi tattalin arziki da rashin ayyukan yi da cin hanci da rashawa da suka yi wa kasar katutu.

Haka kuma a baya-bayan nan matsalar hauhawar farashin kayayyaki ya sa mutane shiga cikin halin ni-'ya-su. Sai dai gwamnati ta ce tana bakin kokarinta don ganin an shawo kan matsalolin.

Labarai masu alaka