EFCC na tuhumar Shell da ENI da ba da hancin $1.3m

Royal Dutch Shell da ENI Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Royal Dutch Shell da Eni na daga cikin hamshakan Kamfanonin mai a duniya

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya, EFCC, ta shigar da sabuwar kara tana tuhumar manyan kamfanonin mai biyu, wato Royal Dutch Shell da ENI.

Hukumar ta EFCC tana zargin su ne da hannu a wata badakalar cin hanci da ta danganci sayen wata rijiyar mai a kasar a kan kudi dala miliyan 1.3 a shakrarar 2011.

Wannan ce tuhuma ta baya-bayan a wani binciken almundahana mai sarkakiya da ake yi a kasashe da dama.

Hukumar mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati a Najeriya, ta zargi kamfanonin da hada baki da nufin aikata mugun laifi na aiwatar da almundahana a hukumance.

Kamfanin mai na Royal Dutch Shell mallakar kasar Holland dai ya ki cewa komai a kan zargin.

Shi kuwa hamshakin kamfanin mai na Italiya ENI, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce ba a sanar da shi ba game da tuhumar ta baya-bayan nan, amma ya jaddada cewa ya ya yi komai bisa ka'ida a lokacin sayen rijiyar man, wacce ake yiwa kallon daya daga cikin mabubbuga makamashin Najeriya da aka fi fatan samun alheri daga gare su.

Ana tuhumar shugaban ENI da bayar da cin hanci a Nigeria

'Yan Nigeria sun sake kai karar Shell

Babban zargin da ake wa kamfanonin biyu shi ne suna sane da cewa lokacin da suka biya kudin sayen rijiyar man lakadan, za a karkatar da shi ne cikin aljihun wasu tsirarun mutane a matsayin na goro.

A baya dai duka kamfanonin biyu sun musanta zargin da ake musu, suna masu cewa sun biya kudin ne kawai ga gwamnati, kuma ba su san komai ba game da duk wani shiri da aka yi na daban.

A baya-bayan nan ne gwamnatin ta Najeriya ta kwace rijiyar man ta kuma bayar da izinin dakatar da ayyuka har sai an ga sakamakon kararrakin da aka shigar na zargin cin hancin.

A yanzu dai daga kamfanin na Shell har ENI suna shirin daukaka kara.