Boko Haram: Shin za ku goyi bayan hana sa hijabi?

Hijabi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu na ganin hana sa hijabi ba zai zama mafita ga matsalar harin kunar bakin wake ba

A Najeriya, salon da mayakan boko-haram suka runguma na kai harin kunar-bakin-wake ta hanyar amfani da suturar mata musulmi ta hijabi da lullubin himar, na ci gaba da haddasa muhawara a kan ko ya dace a haramta amfani da hijabin na wani lokaci don inganta tsaro.

Ana zargin mahara kan yi amfani da hijabin wajen boye bama-bamai a hare-haren da suke kai wa, wadanda suka yi sanadin mutuwar mutane da dama a shiyyar arewa-maso-gabashin kasar.

Yayin da wasu ke goyon bayan haramta sanya hijabin, wasu kuma na adawa da hakan, suna cewa sutura ce da addinin musulunci ya tanadar, don haka ya kamata jami'an tsaro su tsaurara bincike, maimakon haramta hijabi.

'Ɗan kuka mai jawo wa uwarsa jifa'

'Yan magana dai kan ce ɗan kuka shi ke ja wa uwa jifa!

Yayin da al'ummar Musulmi a Najeriya ke alfahari da suturar mata ta hijabi da lullubin himar, sakamakon yadda yake rufe tsiraici da kare martabar mata.

Babban kalubalen da wannan sutura ke fuskanta shi ne zargin da ake yi cewa mayakan Boko Haram na amfani da ita wajen kai harin kunar-bakin-wake, musamman a shiyyar arewa masu gabashin Najeriya, inda rikicin boko haram din ya fi kamari.

Duk da irin ikirarin da jami'an tsaro ke yi na karya-lagon kungiyar Boko Haram, bincike na nuna cewa idan da wani abin da ke tsole-idon jami'an tsaro da kuma al'umomin da ke yankunan da ke fama da irin wannan harin kunar-bakin-wake a halin da ake ciki, babu kamar bad-da-sawun da maharan ke yi ta hanyar amfani da hijabi.

Wani jami'in kato-da-gora, wato matasan da ke tallafa wa jami'an tsaro a jihar Borno da ya nemi a a sakaya sunansa ya ce, "Muna sa ido sosai a kan maza da mata, sai dai yawanci masu kawo harin su kan saka himar ne wadatacce kuma mai kyau wanda da wuya ka gane su."

'Kayan aro'

A dan tsakanin nan dai, hare-haren da aka kai kan wasu wuraren da ke da jama'a, musamman a birnin Maiduguri sun sa wasu mazauna birnin shiga fargaba idan suka ga bakuwar fuska da hijabi da babban lullubin himar.

Masu sana'a da dama na dari-dari da masu saka hijabin, kamar Habu Madu Bulama ya shaida wa BBC. Lamarin dai ya fara haddasa zazzafar muhawara a kan ko ya dace a haramta amfani da hijabi a yankin.

"Ni dai yanzu ta kai ko fita sallar asuba ba na yi, a gida nake yin ta don rashin tabbas a harkar tsaro," in ji wani mazaunin unguwar Fori.

Amma duk da haka wasu na ganin cewa haramta saka hijabin bai dace ba. Wani mazaunin unguwar Forin ya shaida min cewa, "Ni fa matata ba za ta daina saka hijabi ba, na gwammace na rakata duk inda za ta je da ba a santa ba don gudun zargi."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana yawan kai hare-haren kunar bakin wake a Maiduguri

A ziyarar da tawagar BBC ta kai birnin Maiduguri, ta ga yadda hijabi ya zama ruwan dare a birnin, kasancewar za ka ga mata sanye da shi a lungu da sakon birnin.

Wasa-wasa dai, wannan muhawara ta kai bakin wasu daga cikin dattawan gari.

Alhaji Bulama Mali Gubio, shi ne shugaban kungiyar Dattawan jihar Borno, wanda ya ce matan yankin suna da sutura tun fil-a-zal, kuma babu wani abin damuwa ba ne idan aka haramta hijabi, da ma aro suka yi suka yafa.

"Mu dama can matanmu ba su san mene ne hijabi ba, amma kuma tun fil azal suna yin shiga ta kamala da mutunci da suturun al'adunmu kamar laffaya da gyale da zani, don haka don an hana sawa yanzu ba wani abu ba ne," a cewar Alhaji Bulama.

Sojoji sun dakile wani harin kunar-bakin-wake a Borno

'Ba ruwan hijabi'

Sai dai ba a taru aka zama daya ba. Wasu matan na da ra'ayin cewa harin kunar-bakin-waken da ake fama da shi, ba shi da alaka da hijabi. Malama Fanta Kacalla, ita ce shugabar kungiyar mata musulmi ta karamar hukumar Bama.

Ta ce, "Ba don hijabi ake kai wannan hare-haren ba, ko basu sa hijabi ba su kan kai hare-harensu, don haka tun da ana bincike to sai a dinga bincikar mutane kawai, amma ni ba zan iya daina sa hijabi ba."

Ganin yanda ra'ayoyin jama'a ke cin karo da juna, Ibrahim Isa ya tuntubi Sheikh Ibrahim Mustafa, wani shahararren malamin addinin Musulunci a Maiduguri, don jin yadda yake kallon lamarin a mahangar addini.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

"Hana sa hijab ba shi ne zai yi maganin wannan matsala ba, ko ba hijabi ai dole za a saka sutura," in ji Malam Mustafa.

Ya kara da cewa, "Wani lokaci ma ai mazan ne ke kai harin ba tare da sun sa hijabi, su kan boye bam din a cikin babbar rigarsu yada ba za a ga me suka boye ba."

"Hijabi umarnin Allah ne ba na mutum ba, don haka bin umarnin Allah wajibi ne," in ji shi.

A ganinsa hana sa hijabi ba mafita ba ne, babbar mafita ita ce a kara bai wa jami'an tsaro horo da kuma kayan aiki.

Cikas

Yayin da wasu ke jaddada rawar da jami'an tsaro za su taka wajen tsaurara bincike maimakon hana sanya hijabi, jami'an tsaron a nasu bangaren na cewa rashin kayan aiki na taka musu birki, kuma a haka jami'ansu ke mutuwa yayin binciken.

A Najeriyar dai ba wannan ne karon farko da 'yan kasar ke tabka muhawara a kan haramta sanya hijabi ba.

A bara ma makamanciyar wannan muhawarar ta kaure lokacin da shugaba Buhari, a wata tattaunawa da manema labarai ya ce gwamnati za ta duba yiwuwar hana sanya hijabi idan aka ci gaba da fuskantar harin kunar-bakin-wake, furucin da ya ingiza kungiyoyin addinin Musulunci suka yi caaa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kenan, batun hana sanya hijabi za a iya cewa ya zama alakakai ga mahukunta a matakai daban-daban a Najeriya, sakamakon dangantakar wannan sutura da addini, inda shugabanni ke kaffa-kaffa wajen daukar mataki, suna gudun cewa wasu 'yan kasar za su yi kukan an tauye musu hakkin sanya sutura bisa koyarwar addinin Musulunci.

Yayin da a bangare guda kuma mahara na amfani da jinkirin da mahukunta ke yi wajen lalubo mafita, suna kai hare-haren da ke haddasa asarar rayuka.

Labarai masu alaka