Fitaccen Jarumi Arnold ya ajiye aiki saboda Trump

Arnold Schwarzenegger Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Arnold Schwarzenegger da Trump sun sha yin ce-ce-ku-ce a kan shirin na Apprentice

Arnold Schwarzenegger ya ajiye aikin gabatar da wani shirin talbiji mai suna The New Celebrity Apprentice, saboda a cewarsa shugaba Donald Trump ya ɓata shi.

A wata hira da kafar yaɗa labarai ta Empire, jarumin kuma tsohon gwamnan California ya yi iƙirarin cewa ƙarancin masu kallon shirin na da alaƙa da sunan shugaba Trump a matsayin babban fardusa.

Arnold ya ce zai so ya yi aiki "kan wani shiri wanda ba shi da wannan kwashe-kwashe".

Mista Trump - wanda ya ajiye shirin don yin takarar shugaban ƙasa, ya taɓa yi wa magajinsa da ke gabatar shirin ba'a.

A hirar ta ranar Juma'a, Schwarzenegger ya yi iƙirarin cewa wani gangamin nuna adawa da Trump ta shafukan sada zumunta ya yi tasiri wajen janyo raguwar masu kallon shirin, wanda ya fara gabatarwa a watan Janairu.

"Lokacin da mutane suka gano cewa har yanzu Trump shi ne babban fardusa kuma yana karɓar kuɗi daga shirin, sai rabin mutane suka fara ƙaurace masa."

A cewarsa "Ba laifin shirin ba ne... Saboda duk wanda na gamu da shi sai ya zo ya ce min, 'Ina son shirin... amma sai in kashe saboda matuƙar zan karanta sunan Trump, to babu ni a ciki!'

"Lokaci ne da ake fama da rarrabuwar kai yanzu kuma ina jin shirin ya samu kansa a cikin wannan al'amari," in ji shi, ya ƙara da cewa ba zai yi ba idan aka ce ya sake gabatar da shirin."

Sau tari, Arnold Schwarzenegger na karawa da Donald Trump a kan shafin Twitter.

Amurkawa miliyan 20 ne ƙa'ida suke kallon shirin a shekarar da aka ɓullo da shi, kafin adadin ya yi ƙasa zuwa miliyan shida karo na ƙarshe da Trump ya gabatar, daga bisani ma adadin ya sake yin ƙasa zuwa miliyan biyar.

Labarai masu alaka