Dubban mutane na zanga-zanga a Jamhuriyar Nijar

Niger Republic Hakkin mallakar hoto Sule Niamey
Image caption 'Yan adawa na ja da gwamnati a Jamhuriyar Nijar

Dubban magoya bayan kawancen jam'iyyun adawa na FRDD a Jamhuriyar Nijar suna zanga-zanga a harabar majalisar dokokin kasar dake Niamey, babban birnin kasar. Tun da safiya masu zanga-zangar suka fito.

Masu zangar-zangar dauke da kwalaye dauke da rubuce-rubuce, zun hada da maza da mata. Suna dai zargin gwamnatin kasar da rashin iya mulki da kuma yadda suka ce matsalar cin hanci da rashawa ta yi wa harkokin gwamnati katutu.

Kawancen adawar sun bayar da misali da wata almundahana da ake zargin ministan kudin kasar Hasoumi Masa'udu ya yi da kudade biliyar dari biyu na CEFA a wata harka ta ma'adanin Uranium, a lokacin yana matsayin darakta a fadar shugaban kasa.

Sun ce gwamnatin ta ki yin komai game da wannan zargi, duk da kiraye-kirayen da ake yi.

Hakkin mallakar hoto Sule Niamey
Image caption Gwamnati na cewa zarge-zargen da masu zanga-zangar ke yi marasa tushe ne

Rahotanni na cewa an dade ba a yi irin wannan zanga-zangar ba a kasar ta Nijar, ta fuskar yawan jama'a da suka fito. To sai dai tana gudana cikin lumana kamar yadda aka tsara.

Kawancen na FRDDR ya kara da cewa akwai kuma wasu lamuran rashawa da dama a harkokin gwamnati yayin da talakawa ke shan bakar wahala wajen samun abinda za su ci da biyan sauran bukatunsu na yau da kullum.

Sakataren watsa labarai na jam'iyyar MODEN Lumana wadda ke cikin kawancen 'yan adawar, Muhammane Laouali Salisou, ya ce za su ci gaba da matsa wa gwamnati lamba kan matsalolin da kasar ke fuskanta.

Masu zanga-zangar sun zargi gwamnatin Muhammadou Issoufou da nuna halin ko oho kan tabarbarewar lamura a kasar. Sun kuma bukaci majalisar dokokin kasar da ta rika taka wa shugaban birki.

To sai dai gwamnatin Nijar din da magoya bayanta sun bayyana zarge-zargen da 'yan adawar ke yi a matsayin marasa tushe, kuma neman bata wa gwamnatin suna ne kawai.