Gwamnatin Obama ta yi mini sata - Trump

Trump Obama
Image caption Obama ne ya mika wa Trump ragamar shugabancin Amurka a watan Janairu amma ana jin ba su jituwa

Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi gwamnatin Obama da ta shude da satar bayanan wayarsa a ofishinsa na Hasumiyar Trump dake birnin New York, a lokacin yakin neman zaben da ya gabata.

A wani jerin sakwannin Tweeter, Mista Trump, bai bayar da wata shaida ko hujja ba game da zargin, amma ya bayyana satar bayanan wayar tasa a matsayin mummunan al'amari.

Ya kuma bayyana Barack Obama a matsayin ''mutumin banza''.

Rahotannin kafofin watsa labarai na baya-bayan nan sun nuna cewa hukumar bincike ta FBI ta nemi takardar izini domin sa ido a kan mukarraban Trump wadanda ake zargi da yin huldar da ba a saba yin irinta ba da kasar Rasha.

Kawo yanzu dai fadar gwamnatin Amurka bata ce uffan ba, kana fishin Mista Obama bai mayar da martani ba.

To amma wani 'dan majalisar wakilan Amurka na jam'iyyar Dimokurat ya ce shugaban kasa baya bayar da izinin satar bayanan sadarwar waya, alkalai ne kan yi.

A lokacin yakin neman zaben shugaban kasa, an samu rahotanni a watan Mayun bara cewa ma'aikatan Mista Trump sun ce suna jin ana satar tatsar bayanai a ofisoshinsu dake ginin na Hasumiyar Trump a birnin New York.

A watan Janairu ne Mista Obama dan jam'iyyar Dimokurat, ya mika wa Mista Trump, dan jam'iyyar Republican shugabancin Amurka.

Labarai masu alaka