BH: 'Mata masu hijabi na firgita mu'
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Boko Haram: 'Mata masu hijabi na firgita mu'

Salon da mayakan Boko Haram suka dauka na kai harin kunar-bakin-wake ta amfani da hijabi na ci gaba da haddasa muhawara a kan ko ya dace a haramta sa shi don inganta tsaro a Najeriya.

Wasu daga cikin mazauna birnin Maiduguri, mahaifar kungiyar, sun shaida wa BBC cewa suna fargaba da zarar sun ga mace sanye da hijabi.

Sai dai wasu na ganin cewa ba zai yi wu a hana sanya hijabi ba saboda abu ne da addini ya umarta, kuma ba shi ne matsalar ba.

Saurari rahoton Ibrahim Isa na musamman kan wannan batu a saman wannan shafi.

Labarai masu alaka