Mexico ta fara taimakon 'yan kasar da ke Amurka

'Yan sandan Amurka a bakin aiki
Image caption Duk bako dan ciranin da aka samu da aikata laifi za a tasa keyarsa zuwa gida

Kasar Mexico ta bude cibiyar taimakawa 'yan kasar mazauna Amurka, a birane 50 na kasar a wani yunkuri na kare su daga tsauraran matakan da gwamnatin Shugaba Donald Trump ta dauka kan baki 'yan ci-rani.

Ministan Harkokin wajen kasar, Luis Videgaray ya nuna damuwa game da take hakkin 'yan kasar da ya ce ana yi a Amurka.

Sai dai ya jaddada cewa cibiyoyin ba za su bai wa wadanda suka shiga Amurkar ba bisa ka'ida ba wata kariya.

Mexico na nuna damuwa kan sabbin dokokin da Mista Trump ya gabatar a watan da ya wuce kan baki 'yan ci-rani, wanda ka iya shafar yawancin 'yan kasar mazauna Amurka.

Mista Trump ya bukaci jami'an gwamnati su hada karfi da karfe da 'yan sanda da jami'an shige da fice dan fitar da sabbin matakan da ya kamata a dauka na tasa keyar baki 'yan ci-rani zuwa kasashensu.

Miliyoyin 'yan Mexico da ke Amurka na fuskantar barazanar mayar da su gida a karkashin sabbin dokokin shige da ficen.

Shugaba Trump ya kuma sha alwashin gina katanga tsakanin Amurka da Mexico domin hana bakin haure shiga kasar.

Labarai masu alaka