India: Jirgin mata zalla ya tashi a 'karon farko'

Mata ma'aikatan Air India
Image caption Ko a baya kamfanin Air India ya kebe wani bangare a cikin jirginsa dan mata zalla

Kamfanin jiragen sama na Air India ya ce a karon farko jirginsa ya yi balaguro daga kasar zuwa birnin San Francisco na Amurka, inda mata zalla suka kasance ma'aikatan jirgin.

Jirgin samfurin Boeing 777 ya keta tekun Pacific akan hanyarsa ta zuwa Amurka, kuma tun daga kan matukin jirgin har zuwa ma'aikatan kula da jin dadin matafiya mata ne.

Kamfanin Air India ya ce hatta ijiniyoyin da ke duba lafiyar jirgi kafin ya tashi, da masu dura mai, da masu bada hannu mata ne babu namiji ko guda a ciki.

Air India ya kara da cewa a wani bangare na shagalin bikin ranar mata ta duniya, da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe a kowacce ranar 8 watan Maris, ma'aikatan kamfanin mata zalla za su sa ke yin balaguro irin wannan.

A watan Janairun da ya gabata, kamfanin ya fara kebe wani bangare a cikin jiragensa da mata ne kadai za su zauna.

Hakan dai ya faru ne saboda korafin da wasu suka yi cewa mata a cikin jirgi kan yi wata kungiya dan yin hira a tsakaninsu.

Don haka kamfanin ya yi kira da a sanya shi cikin littafin nan da ake sanya abubuwan da suka shahara da kuma na ban mamaki a tarihi wato Guinness World Record.

Labarai masu alaka