An rataye 'yan ta'adda 15 a Jordan

Ofishin diflomasiyyar Jordan a Iraqi
Image caption Gwamnatin Jordan ta dade ba ta yanke hukuncin kisa irin wannan ba

Hukumomin kasar jordan sun rataye fursunoni 15, ciki har da mutane 10 da aka samu da aikata ta'addanci.

Da safiyar yau ne aka rataye dukkan fursunonin 'yan kasar, a gidan kaso da ke babban birnin Amman.

Sauran mutane 5 din an rataye su saboda samun su da laifikin cin zarafi ta hanyar yin fyade.

Shekaru da dama kenan da Jordan ba ta yanke hukunci irin wannan ba.

Cikin wadanda aka taraye, har da masu hannu a harin da aka kai ofishin jakadancin kasar da ke birnin Bagadaza a shekarar 2003, da wanda aka kai wa masu yawon bude ido a Jordan a shekarar 2006, da harin da aka kai wa jami'an hukumar leken asiri a sansanin Baqaa a bara.

Masu aiko da rahotanni sun ce, gwamnati ta sauya manufofin ta da irin hukuncin da ake yankewa wadanda aka samu da laifi irin wannan, saboda yawaitar aikata muggan laifuka da ake yi a kasar, da kuma yaduwar ayyukan kungiyoyin 'yan ta'adda irinsu ISIS a kasashen Syria da Iraqi.

A bangare guda kuma, kungiyar kare hakkin bil'adam ta Amnesty International ta yi Allawadai da hukuncin.

Labarai masu alaka