Ko kun san dalilin da ya sa muke son alawa?

An sake sabunta labarin bayan fara wallafa shi ranar 5 ga watan Maris 2017.

Yara kanana na son alawar cakulan
Bayanan hoto,

Daddadan kamshin alawa na daga cikin dalilan da ke daukar hankalin 'yan adam

Da zarar an tambayi wani dalilin da ya sa muke shan alawar cakulan, abu na farko da za a fara fada shi ne saboda tana da dadin dandano a baki.

To amma ba wannan ne kadai dalilin da ya sa muke shan alawar ba, watakil saboda sinadarin carbohydrates mai gina jikin dan adam na cikin abubuwan da aka yi amfani da su wajen hadata.

Ina matukar kaunar alawar cakulan, duk lokacin da na fara sha, ba na daina wa har sai wadda ke hannu na ta kare.

Bantaren alawar ko rabi sam ba ya isa ta, kai hatta a gidan mu an san yadda na ke kaunar alawa dan haka ne ma idan an siyo to ya zama lallai a boye ta in ba haka ba sai na shanye ta.

Ko mene ne dalilan da suka sanya cewa aka samu wasu nau'in abinci da mutane ba sa iya dauke kan su akai?

Kuma wacce alaka ce tsakanin irin nau'in abincin da alawa da mutane ba sa taba dauke idanuwansu daga kai?

Ga amsar binciken da James Wong ya yi kan haka

Bayanan hoto,

Da zarar alawar cakulan ta taba harshen dan adam, ta ke fara narkewa

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ana samar da alawar cakulan ne daga 'ya'yan gahawa, wanda dubban shekaru kenan da ake shukawa a kasar Amurka.

'Ya'yan gahawa suna fitar da wani kamshi mai dadin gaske, da kuma dan daci idan aka dandana, dalilin kenan da kafin a yi amfani da shi dan samun gahawa da ake sha kamar shayi.

Shi kuma wanda ake sarrafawa dan yin alawar cakulan sai an bare shi daga kwandon shi wanda anan dacin ya fi yawa.

Abubuwan da ake amfani da su wajen hada alawar cakulan da suke sanyawa ta ke wani kamshi na musamman, na daga cikin abinda ke jan hankalin mutane son shan alawar.

Shin akwai wani abu da ya kamata mu sani game da alawar cakulan?

Baya ga dandano mai dadi da alawar ke da shi, da zarar an bare ta daga takardar ko ledar da aka kunshe ta a ciki, aka kuma sanya ta a baki tun ma kafin a gutsira ta ke fara narkewa akan harshe, tare da yin wani laushi a baki.

Wannan yanayin shi ke sanya mai shan alawar nishadi, da annashuwa a lokacin da yake shan ta.

To amma fa, kar mu manta an yi amfani da sikari da abubuwa masu maiko, wajen hada alawar da shi ne ya bata wannan dandanon mai zaki a harshen mu.

Asalin hoton, Thinkstock

Bayanan hoto,

Ruwan nonon uwa na kunshe da wani kaso na sikari da maiko

Adadin sikari da sinadaran da ake amfani da su wajen hada alawa ya kan wuce iya adadin da jikin dan adam ya kamata ya dauka.

Misali a duk lokacin da ka duba bayan kwali ko makunshin da alawa ke ciki za ka ga an rubuta abubuwa kamar haka:

An yi amfani da kashi 20 zuwa 25 cikin 100 na sinadaran maiko.

An kuma yi amfani da kashi 40 zuwa 50 cikin 100 na sikari a ciki.

Ana iya samun sikari daga jikin kayan marmari da muke da su, akan kuma samu maiko sosai a cikin gyada, amma an fi samun dukkan biyun a cikin madara.

Ruwan nonon dan adam dauke yake da sikari da kuma maiko, an yi kiyasin ana samun kashi 4 cikin 100 na maiko a cikin nonon dan adam, da kuma kusan kashi 8 cikin 100 na sikari a ciki.

Haka kuma yawancin madarar da ake shayar da jarirai da ita, ta kunshi abubuwan da aka lissafa na sikari da maiko a ciki.