Boko Haram: Jakadun kwamitin sulhu sun isa Nigeria

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya Hakkin mallakar hoto UN
Image caption Ziyarar wani bangare ne, na rangadin da su ke yi dan ganin yawan barnar da yankin ya fuskanta sakamakon rikicin Boko Haram

Tawagar kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ta isa birnin Maidugurin na Najeriya a wani bangare na ziyar da suke a yankin Tafkin Chadi domin ganin irin barnar da rikicin Boko Haram ya haifar.

Jakadun kwamitin su 15 sha biyar, za su yi ƙoƙarin tantance matsalar ayyukan jin ƙai da Kamaru da Chadi da Najeriya da kuma Nijar ke fama da su.

A baya-bayan nan Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana damuwa kan annobar yunwa da ta ce miliyoyin mutane na fuskanta a yankin tafkin Chadi.

Ana sa ran tawagar za ta tattauna da gwamnan jihar Borno Alhaji Kashim Shettima, da kungiyoyin fararen hula, da shugabannin garuruwan da rikicin ya fi shafa.

Za kuma su kai ziyarar gani da ido wasu daga cikin sansanonin 'yan gudun hijira da ke jihar ta Borno.

A ranar Litinin ne kuma za su isa Abuja, babban birnin kasar, domin ganawa da jami'an gwamnatin tarayya.

Manufar wannan ziyara ita ce ƙarfafa gwiwar shugabannin ƙasashen domin su bijiro da wani bakandamen tsarin tunkarar barazanar Boko Haram a kan iyakokinsu.

Tuni tawagar ta kai irin wannan ziyara kasashen, Chadi da Jamhuriyar Nijar, da kuma Kamaru.

Matakin zai kuma yi ƙoƙarin jawo hankalin ƙasashen duniya kan wannan rikici wanda jakadan Burtaniya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Matthew Rycroft ya ce galibi an kawar da kai daga gare shi.

Labarai masu alaka